22 Faburairu 2017 - 12:21
Taron Goyon Bayan Palasdinu A Tehran Nuna Raunin 'Yan Sahayoniya A Gabas Ta Tsakiya.

Mataimakin Shugaban Kungiyar alwifaq ta Bahrain, ya ce; Taron Wata Dama ce ta Nuna Raunin 'Yan Sahayoniya A Gabas Ta Tsakiya.

Mataimakin Shugaban Kungiyar alwifaq ta Bahrain, ya ce; Taron Wata Dama ce ta Nuna Raunin 'Yan Sahayoniya A Gabas Ta Tsakiya.

Mataimakin shugaban Kungiyar ta alwifaq ta Bahrain, Husain al-Duihy, wanda ya ke halartar taron kasa da kasa na goyon bayan intifada, ya ci gaba da cewa; Jawabin da jagoran juyin musulunci na Iran ya yi, kaifin wuka ne, kuma ya maida hankali ne akan duniyar musulunci.

al-Duihy ya kuma yi suka ga tsarin nuna wariya da ya ke tafiyar da gwamnatin Bahrain akan 'yan asalin kasar da kuma raba wasu da hakkinsu na zama 'yan kasa.

Bugu da kari, jami'in na kungiyar alwifaq ya yi ishara da alakar da ali-khalifa su ke da shi da 'yan sahayoniya a fili da boye, wanda hakan ya bakantawa al'ummar kasar.288